Updated Jun 1, 2026 · v1.16
Ingantattun zikirori da addu'o'i daga Alƙur'ani da sunna
Adhkar Hausa manhaja ce ta Ilimi wacce aka tsara domin sauƙaƙawa musulmai samun Zikirori da Addu'o'i cikin harshen Hausa. Manhaja ce da ta ƙunshi ingantattun zikirori da addu’o’i daga Alƙur’ani da Sunna, waɗanda aka tattaro daga sahihan littattafai. ✨ Abubuwan da zaka samu a cikin manhajar: 1. Zikirin safiya da maraice 2. Zikirin da ake yi a cikin salla 3. Zikirin bayan an yi sallama daga salla 4. Littafin Hisnul Muslim 5. Falaloli: - Falalar zikiri - Salati ga Annabi (SAW) - Istigfari - Tasbihi, tahmidi, tahlili, da takbiri, - Da sauransu 📌 Siffofi na musamman (Features): 1) Addu’o’i cikin larabci da fassarar Hausa 2) Audio don sauraron addu’o’i ba tare da amfani da data ba (offline) 3) Neman addu’a cikin sauƙi ta hanyar rubuta sashi na sunan ta 4) Kalar allon screen mara haske domin kare ido 5) Tura addu’a kai tsaye zuwa wasu manhajoji Da sauran su... 🌱 Za mu ci gaba da ƙara sabbin abubuwa lokaci bayan lokaci in shaa Allah. 🤝 Ka yada ka samu lada: Ka turawa ƴan’uwa Musulmai wannan manhaja domin su amfana.
3 years on Google Play
This app isn't currently appearing in any tracked top charts.